Archive for March, 2010


TAMBAYOYI

Mene ne muhimmancin motsa jiki? Kuma wane lokaci ya dace ayi shi?

-N.I, Ringim.

Ba shakka motsa jiki akai-akai na daya daga cikin hanyoyin samun koshin lafiya. Bincike dabam-dabam ya nuna cewa motsa jiki kan hana cututtuka irin na zuciya da na mutuwar barin jiki aukuwa, ta hanyar kona man cholesterol, da rage hawan jini, da rage siga a jiki ga masu ciwon siga da ma wadanda basu da ciwon. Wato dai a hannu daya motsa jiki riga-kafi ne babba daga ciwon siga, ciwon zuciya, ciwon hawan jini, ciwon mutuwar barin jiki, wasu ciwukan na daji wato kansa, ciwon baya, ciwon jiki, ciwon damuwa na depression, ko na kasala da ma wasu da dama. A daya hannun kuma motsa jiki kan yi maganin duk wadannan ciwuka idan basu yi nisa sosai ba.

Binciken suka kuma ci gaba da nuna cewa mai motsa jiki akai-akai bayan annashuwa da zai rika ji a ransa, da kuma jin karfin jiki ta hanyar kara kwarin kasha, ana sa ran kuma zai samu karin shekaru a duniya.

A mafi yawan lokuta mutane sun fi jin dadin motsa jiki da safe, amma masana sun tabbatar da cewa ko da wane lokaci ma ana iya yi don za a iya samun duk fa’idojin da ake samu da safen. Ba wai kawai ka zage da tikar gudu a fili shine kawai motsa jiki ba, a’a idan ka yi tafiyar minti 45 a kowacce rana ko da mintina 15 sau uku (wato ya dai tashi minti 45) indai za ka yi a kullum, to kana daya daga cikin mutane masu motsa jiki.


An gwada siga na a asibiti ya nuna 8.8 aka ce ina da ciwon siga aka bani magunguna da wasu ka’idojin cin abinci. Da na gama na ‘yan kwanaki sai na koma aka gwada aka ga ya dawo 5.5. A wancan lokaci bana cin wasu kalar abinci amma yanzu ina cin komi kuma sigan baya wuce 5.0 don ya nuna hakan fiyen da sau goma. To shin ya abin yake ne don ance ba a warkewa.

-Musa.

Cewa ko kana da ciwon siga ko baka dashi ya danganta da lokacin da aka dau jinin, wato da safe kafin kaci abinci ne ko kuwa? Kuma idan da safe ne sau daya kawai aka gwada ko sau da dama? Wato wani gwaji mai suna OGTT da za a dau siganka a gwada duk bayan awa biyu biyu shine zai tabbatar kana da ciwon siga ko a’a, kuma idan ba a dau fitsarinka an gwada ko yana dauke da siga ba, ba za a iya tabbatarwa ko kawai siganka ne yayi sama a wannan lokaci ba.

Amma da yake ciwon siga iri-iri ne, watakil naka irin wanda wani abu ke jawo shi ne kamar kiba da wasu cutukan (wanda ake kira secondary diabetes) wanda shi yakan warke gaba daya. Amma idan har kana da gadon ciwon siga wato idan akwai mai irinsa a gidanku tunda kace ku uku ne kuke da irin ciwon, to shi baya warkewa sai dai ya lafa. Kuma idan ya lafa ka kan iya rayuwarka kamar maras ciwon in dai ka bi ka’idojin da likitan ya baka.

Shawara dai itace idan akwai mai ciwon a dangi, ka gayawa likitanka ayi gwajin OGTT da na fitsari a tabbatar.


Nine mai syphilis kuma na je an min gwajin VDRL an ce non-reactive. Shin kana ga har yanzu da sauran wannan ciwo?

-Y.M, Dambatta.

A’a tunda gwaji ya tabbatar babu ciwon kuma ba ka da wasu alamu sai na wannan tabo to ciwo ya tafi kenan kuma shima tabon a hankali da sannu zai baje.


Duk lokacin zafi tafin hannuna da na kafata sai sun bambare (sai sun yi saba). Me yake kawo hakan?

-Bakari, Maiduguri


To saba iri-iri ce itama akwai ta gado akwai kuma ta canjin yanayi. Yawanci duka gado ake don haka da wuya kenan ciwon ya tafi baki daya, sai dai a rika shafa mai mai karawa fata taushi da lafiya wato irin man na mai dauke da sinadaran vitamin na rukunin A da E.


Mene ne amfanin tsarki da toilet paper kafin ayi da ruwa?

-Shafi’u.


To shidai bayan gida kashi 90 cikin dari duk kwayoyin cuta ne wadanda nan da nan za a iya sawa a abinci ba tare da an sani ba. Don haka idan aka yi amfani da wani makari kamar toilet paper aka share sarai za a iya kiyaye kwasar kwayoyin cuta da dama a hannun, musamman a cikin farce ko kumba. Daga nan a sa ruwa da sabulu a wanke ragowar. Shima hannun shi yasa ake sa sabulu ko toka a wankesu sarai.

Kaga da zamu rike wannan dabara kadai musamman ga masu abincin sayarwa da ‘yan aiki masu abinci a gidajenmu,  da za mu rage ciwon tafot kwarai da gaske tunda da hannun da ya taba bayan gida wanda ke dauke da kwayar cutar ake yada shi wannan ciwo

HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON SANKARAU

HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON SANKARAU

A watan nan da ya wuce an bada labarin bullar ciwon Sankarau a makociyarmu kasar Ghana inda aka tabbatar akalla mutane 140 sun kamu da wannan ciwo. Kwatsam sai kuma aka ji hukumomi ma a Najeriya na bada bayanin bullar wannan ciwo.

A irin wannan yanayi mai shigowa na zafi wanda kuma ya zo lokacin da aka samu ‘yan gudun hijira na fadace-fadace, sankarau kan yi barna idan ba a dauki matakan kariya ba. Don haka yana da kyau mu dan kara yin bita ga daidaikunmu akan hanyoyin da zamu bi wajen kare kai daga wannan ciwo.

Ciwon sankarau wani nau’in ciwo ne da kwayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lullube kwakwalwa da lakar wuya da gadon baya watomeninges a turance. Akwai nau’o’in ciwon sankarau daban-daban wanda kwayoyin cuta iri-iri ke kawowa. Kwayoyin cutar bacteria ne da ake kira Neisseria meningitidis ke kawo nau’in sankarau din da muka fi sani.

Su wadannan kwayoyin cuta suna nan a cikin iskar da muke shaka mai zafi. Hasali ma kashi daya cikin biyar a cikinmu masu lafiya na dauke da wadannan kwayoyin a hancinmu da makogwaronmu bamu sani ba. Ta haka ake yadasu in anyi kaki an tofar ko kuma ta iska a wuri mai cinkoso. Kwayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi. Don haka da wuya ayi sankarau lokacin sanyi.

Idan aka shakesu ta hanci kwayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashesu ya kai mayafin kwakwalwa. Nan da nan alamomin cutar zasu bayyana.


Alamomin Ciwon

Ciwon sankarau yafi kama yara ‘yan shekara 5-10, amma a lokaci na annoba zai iya kama kowa. Alamomin ciwon sankarau suna da yawa. Da farko dai akan ji

  1. Ciwon kai mai tsanani
  2. Zazzabi, sai
  3. Sankarewar wuya

Da zarar an ji wadannan alamomi na farko sai ayi maza a garzaya asibiti mafi kusa. Idan an dade ba je asibiti ba, za a ga mutum ya fara

  1. Amai
  2. Rashin son ganin rana ko haske
  3. Wasu kuma sukan suma
  4. Daukewar numfashi akai-akai wanda yakan sa a rasa mutum

Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo?

1.      A irin wannan lokaci, ayi nesa da jama’a musamman wajen taron suna ko biki ko daurin aure ko kallon kwallo, ko kuma a yi taron a waje

2.      A rika kwanan waje a gidan yawa ko wurare irin su makarantun kwana, ko wuraren samun mafaka na ‘yan gudun hijira irinsu bariki, da ma sauran wurin kwanciya na mutane da yawa kamar gidajen kaso.

3.      A tabbatar dakin barci na da tagogi bude a kalla biyu masu kallon juna. Idan taga daya ce abar kofa bude musamman idan mutane fiye da biyu ne a dakin

4.      A je cibiyoyin alluran riga kafi domin a karbi allurar riga kafin ciwon sankarau

5.      A face majina inda ya dace ba a cikin mutane ba

6.      Idan wani na kusa a gida ko wurin aiki ya kamu da ciwon to duk mutanen wurin ko da basu yi ciwon ba, su je su karbi magani a asibiti.

7.      A yi saurin kai wanda ya kamu da wannan ciwon asibiti don gudun yada cutar ko ya galabaita.

8.      Cin abinci mai gina jiki da shan kayan itatuwa na marmari masu tsabta musamman ga yara don kara karfin garkuwar jiki masu iya kashe kwayoyin cutar tun kafin su isa kwakwalwa.

AMSOSHIN TAMBAYOYI


Ina fama da fitsarin jini, na sha magunguna amma Allah baisa ya tafi ba

-A. S. Mukhtar.

Idan da kaje asibiti da tuni an gano abin da ya kawo hakan watakil kuma da tuni an fara magani. Bari in kara nanata maka abubuwan da kan kawo fitsarin jini, wadanda duk sai an dan yi binciken jini da fitsarin kafin a ce daya daga cikinsu ne;

1.     1. Wankan  rafi na kuruciya wanda kan jawo ciwon tsargiya, ciwonda wasu tsutsotsi kan rika kartar fatar mararka har tayi jini ka rika gani a fitsari

2.      2. Wanda idan aka sha maganin praziquantel bai tafi ba, to  yakan iya zama kari ko tsuro a cikin mafitsarar wanda kan sa ka rika ganin jini

3.      3. Idan kuma ka taba yin ciwon sanyi, wasu kwayoyin cutar kan makale a bangon mararka suna karta har wurin yai jini ka rika ganinsa a fitsari

4.      4. Sai kuma ciwukan koda ko shan magunguna barkatai masu sawa koda illa, wanda kansa koda ta rika jini yana kwaranyowa a fitsari

5.      5. Kumburi ko ciwon daji na wata ‘yar halitta a karkashin marar maza da ake kira prostate gland musamman idan ka ba shekaru hamsin baya ko kuma fitar fitsarin sai an yunkura sosai.

Da dai ciwuka iri-iri da sai anyi bincike marasa tsada kafin a dau mataki walau na magani ko na tiyata.


Ni kuma na taba yin ciwon sanyi ne na syphilis an ba ni magani a asibiti na sha na warke amma har yanzu akwai wani tabon ciwon kan kaciyata duk da dai ba ya ciwo. Ina son Karin bayani.

-Y.M. Dambatta da D.L.M

To wannan tabo in dai likitanka ya tabbatar kana da syphilis shi a likitance muke kira gumma kuma alama ce ta cewa ciwon ya shiga mataki na uku wato da alama bai tafi ba, domin mai wannan ciwon ana so bayan anyi masa magani da allurai, ya koma bayan wata shida da bayan shekara daya da bayan shekara biyu a sake wannan gwajin na farko da ake kira VDRL a tabbatar kwayoyin sun mutu.  In ba su mutu ba sai an sake allurai. Sannan kar ka manta idan kana da iyali ka tafi da matarka itama ayi mata gwajin VDRL.

Follow

Get every new post delivered to your Inbox.