Latest Entries »

YADDA AKE GADO

Qwayoyin halittu na gado sune ke da alhakin yada kamanni da siffofi da cutukan gado a tsakanin iyali ko ma cikin jinsi. Su waxannan qwayoyin halittu masu daukar gado, su ake kira chromosomes .

Da farko dai ya kamata mu san cewa kowane ruwan xa namiji da qwan mace na dauke da qwayoyin halittun gado guda ashirin da uku, waxanda idan sun haxe sun zama xan tayi za su zama dan na dauke da arba’in da shida kenan. A jikin wadannan halittu arba’in da shida ne ake samun masu dauke da siffofin da yaro yakan gada daga mahaifi ko mahaifiya. Siffofin sun haxa da namiji ko mace, tsayi ko gajarta, qiba ko siranta, fari ko baqi, haske ko duhu, qaton kai ko qaramin kai, qarfi ko rauni, qin ji ko salahanci, da ajin jini, da yanayin jerin haqora da dai sauransu. Ban da siffofi kuma, har da masu dauke da gadon cutuka. Akwai cutuka da dama masu bin zuri’a waxanda muke kira cutukan gado, waxanda idan akwai mai su a zuri’arka kaima zaka iya samu. Suna nan sun fi dari, amma bari mu lisssafo muhimmai daga cikinsu:

  1. Ciwon Suga
  2. Hawan Jini/Ciwon Zuciya
  3. Tavin hankali
  4. Amosanin Jini
  5. Sanyin Qashi
  6. Ciwon Daji na Mama
  7. Ciwon Daji na Mahaifa
  8. Yankakken leve

 

Ya kamata kuma mu san cewa qwayoyi masu xauke da wasu siffofi a mafi yawan lokuta (wato a kashi 75 cikin dari) sun fi na wasu siffofin qarfi. Misali, qwayoyi masu ba da jinsin mace, da masu ba da tsayi ko farar fats sun fi masu ba da namiji da masu ba da gajarta da duhu qarfi. To yayin da namiji mai tsayi ya auri mace mai gajarta ko mace mai tsayi ta auri namiji mai gajarta, qwayoyin tsayi sukan danne na gajarta, ta yadda za a samu yaro mai tsayi ko madaidaici. Amma da wuya a samu gajere. Kusan haka zancen yake idan duka masu tsayi ne, ta yadda a iyaye masu tsayi da wuya a samu da gajere (sai dai idan a kakanni akwai). To da ace kuma duk ma’auratan gajeru ne fa? To ‘ya’yansu kusan duka gajarta za su yi (sai dai fa idan a kakanni akwai dogo). Wannan ce ma ta sa a auren farin mutum (farar fata) da baqar fata, kan haifar da samun farin fata ba baqi ba saboda a tsarin gado farar fata ta fi baqa qarfi.

Akwai siffofi na zahiri akwai kuma na badini. Wato sauran halaye ko siffofi da muke dauke da su wadanda ba su fito fili ba suna cikin waxannan halittu a voye har sai an hayayyafa ake ganewa. Misali, gajerun mutane waxanda xayansu ke dauke da qwayar halitta mai siffar tsayi za su iya samun da ko ‘ya mai tsayi. Wannan shi kuma shine gado na wurin kakanni kenan.

Ya kamata kuma mu san cewa wurin zama da yanayin qarfin aljihu da wasu al’adu suna iya yin tasiri akan qwayoyin halittu na zahiri ta yadda sukan rikide idan aka ba su wani lokaci. Wato idan mazaunar ‘ya’ya da iyaye daban-dabam ce, (kamar a ce ‘ya’ya na birni iyaye na qauye) to za a iya ganin bambancin kamanni da juna. Wani babban misali mai nuni da hakan kuma shine idan aka haifi ‘yan tagwaye masu kama daya, aka raba mazauninsu (misali aka kai daya qasar larabawa ko ta turawa, aka bar daya a nan gida), bayan kamar shekaru ashirin idan an gan su a tare sai an yi da gaske kafin a iya cewa ‘yan gida daya ne ma ballantana a gane ‘yan biyu ne. Idan da a ce kuma duka biyun za su rayu a wuri guda, dole bayan shekara ashirin a ga ba su da wani bambanci na kuzo-mu-gani.

Irin wannan ilmi yana da muhimmanci qwarai da gaske musamman a wajen alqalanci, kamar wajen rabon gado ko raba rigimar ‘ya’ya. A qasashen da suka ci gaba, a rikici irin na gado bayan rasuwar wani hamshaqin mai arziki, mutane da dama suka zo a matsayin magada. Anan ana kiran masana kimiyyar gado su fayyace ko shin wane dan wane ne, ko kuma a’a. Hanyar farko da ake bi a gano shine na kalar jini ko ajin jini. Da yake jini an kasafta shi kashi huxu, idan an riga an san ajin jinin uban da na uwar, ajin jinin yaron dole ta dauko na daya daga cikin iyayen. Idan yayi dabam to ba dan su bane. Haka ma ko da ta yi daidai, akwai mataki na gaba da ake iya dauka domin tabbatarwa.

Waxannan qananan qwayoyin halittu masu dauke da gado har ila yau sukan bambanta daga jinsi zuwa jinsi, sukan kuma yi kamanceceniya a tsakanin jinsi daya. Misali, Jinsin Hausawa na da nashi kamanni, na Fulani ma haka. Ta irin wannan ilmi ne kuma yawanci fitattun baqaqen qasar Amurka suka gano jinsunsu na asali da kuma inda suka fito a wannan Nahiya ta Afirka. An gwada qwayoyin halittun gadon ‘yan wasan qwallon tanis dinnan na Amurka wato Serena da Venus Williams da na iyayensu an gano sun fi kama da na Yarbawa. Wasu kuma sun gwada an ce sun fi kama da na mutanen qasar Afirka ta kudu, wasu da dama kuma an gwada an ga sun fi kama da na mutanen qasar Sinigal da dai sauransu.

Image

‘AN KAWAR DA CUTAR KURKUNU A WANNAN KASA’

A yi mini bayani akan cutar kurkunu. Ta yaya mutum zai gane yana xauke da ita kuma ta yaya zai kare kansa idan ba shi da ita?

Daga Maloli, Kano

Amsa: Wannan tambaya taka ta zo a kan gaba, wato a daidai lokacin da hukumomin lafiya na kasa da ma na duniya a karshen shekarar da ta gabata suke iqirarin cewa a yanzu an kawar da wannan ciwon gaba-daya daga kasar nan. Hukumomin suka kara da cewa yau shekaru uku kenan ba a kawo musu rahoton wannan ciwo ba, kuma suma basu ga mai wannan ciwo ba a tsawon wannan lokaci. Don haka suke dakon manyan jami’ai na kasa da qasa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) domin su ba wa kasar nan takardar shaidar cewa an kawar da wannan cuta baki daya daga cikinta.

Tun cikin shekarar 2005 aka sa cewa Najeriya da sauran kasashe 5 (Sudan ta Kudu, Mali, Ghana, Ethiopia, da Chadi) wadanda suke da annobar wannan ciwo za su ga karshen wannan ciwo amma abu ya faskara. Domin a halin da ake ciki har yanzu akwai labarin wannan ciwo a Sudan ta Kudu da Chadi.

An fara yaki da wannan ciwo ne tun kimanin shekaru ashirin da suka wuce da kudin da kungiyar tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter ta samar. A lokacin kasashen Indiya da Pakistan, da Yemen duk suma suna fama da wannan annoba, amma a cikin ‘yan shekaru kadan su suka ga bayan ciwon. A wannan kasa a wancan lokaci babu inda ba a samu bullar ciwon ba, Kudu da Arewa.

A yanzu haka hukumar da ke da alhakin kawar da wannan ciwo a kasar nan wato Carter Foundation da ke da hedikwata a Jos ta saka ladan kudi na kimanin Naira dubu ashirin da biyar (N25,000) ga duk wanda ya kawo rahoton ganin mai wannan ciwo. Bari mu zayyana alamun ciwon ko da zaka dace da wannan lada:

 

Cutar kurkunu ciwo ne da wasu qwayoyin cuta suke kawowa. A gurbataccen ruwa mai dauke da kwayayen kwayar cutar ake daukar ciwon. Don haka za a fi ganin ciwon a karkara, kuma yawanci a garuruwan da suke da rafi a kusa da su.

Idan kwayayen suka shiga ciki, sai su zama macijin ciki. Daga nan ne tsutsar take saukowa kafa ta huda wajen agara ko idon sawu ta fara fitowa (za a ganta fara kuma doguwa a idon sawu), wurin kuma ya zama gyambo. Idan ta fara fitowa sai tayi kwanaki kan ta gama fitowa. Don haka a samu tsinke a nannade ta a jiki a rika janyo ta a hankali ba a lokaci daya ba kar ta tsinke, don in ta tsinke sai anyi tiyata an ciro ta. Kafar takan kumbura fiye da ‘yar uwarta ta yi ta ciwo.

 

HANYOYIN KARIYA

  1. A tace, kuma a bar ruwan rafi ko na rijiya mara zurfi ya kwanta, sannan in da hali a dafa kafin a sha.
  2. A rika wanke hannu da sabulu bayan an yi bahaya saboda kwayayen kan zauna a hannaye
  3. A rika kula da yara sosai kar suci kasa, a kuma rika yawan wanke musu hannuwa da sabulu duk lokacin da suka je wasa suka dawo
  4. Akai mai ciwon kurkunu asibiti mafi kusa ko a sanar da hukuma mafi kusa don daukar mataki
  5. A guji ba haya a kusa da magudanan ruwa ko gonaki ko fadamu saboda gudun yada kwayayen
  6. Dole hukumomi musamman na qananan hukumomi su ci gaba da samar da ruwa mai tsabta kamar rijiyoyin burtsatse ga jama’arsu

Hanyoyin Kariya Daga Saran Maciji

A Najeriyarmu ta arewa an fi samun macizai a jihohin Arewa maso gabas irin su Bauchi da Gombe da Taraba da Pilato, musamman a garuruwan Billiri, da Kaltungo da Alkaleri da Langtan da makwabtansu. Akan samu ma a Borno da Adamawa da kauyukansu. Ko a bana ma a wadannan yankuna an samu karuwar wadannan macizai wadanda aka yi hasashen cewa daga Kasar Kamaru suka shigo sakamakon ambaliyar ruwa da ya biyo dasu nan.

An fi samun wannan matsala ta sarar maciji a tsakanin Manama da makiyaya da mafarauta da masu wasa da maciji.

Macizai masu sara da dafi ba su kai marasa dafi yawa ba, domin da yawa za su iya yin sara ba tare da sun harba dafi ba. Haka nan ma akwai irinsu mesa wadda ba ta sara sai dai ta kama mutum ta nannade a jikinsa ta matseshi ta yadda zai kasa numfashi, har ya ce ga garinku.

 

Alamomin sarar maciji

Yawanci duk wadanda maciji ke sara maza ne ba mata ba, kuma an fi samun wannan matsala a daji ko a gona. Mutumin da maciji mai dafi ya harbeshi za a ga ‘yar kafa ko tsaga a fatarsa ta inda dafin ya shiga, akan ga jini a wurin saboda yawanci dafin macijin kan tsinka jini, jini ya yi ta zuba ta kafafe da dama ya qi tsayawa. Za a ga jinin har ta baka, a wasu lokuta. Sauran alamun sun haxa da firgita da dimaucewa saboda ba tsammani yawanci abin ke faruwa. Mutum kan iya kasa motsi idan dafin ya shiga jijiyoyin laka, a wasu lokuta ma numfashi gagara yake.

A yawancin lokuta wurin da akai saran ba ya wani zogi, sai dai idan a ido aka fesawa mutum dafin nan da nan zai ji radadi ya fara gani dusu-dusu, idan ba a dau mataki da wuri ba ma har makanta dafi a ido kan sa.

Yana da kyau idan an ga macijin a kashe shi a tafi da shi asibiti domin a ba da maganin karya dafin wannan macijin. Idan kuma ba a ga macijin ba za a iya ba mutum maganin dafin kowane irin maciji a asibiti. Wato a asibiti akwai maganin dafi iri-iri, akwai na duka macizai, akwai kuma na macizai daban-dabam. Kusan dukan wadanda akan kai asibiti aka basu allurar da wuri suna rayuwa.

 

Hanyoyin Kariya

  1. Manoma su rika sa takalma masu tsayi da kauri (sau ciki) kamar takalmin ruwa kenan idan za a gona, musamman ma idan a wancan yanki na kasar nan wannan gona take, ko kuma idan fadama ce inda ruwa ke kwanciya
  2. Idan aka ga maciji musamman idan mai dafi ne bai kamata a tanka masa ba, canza hanya ake a kyale shi ya wuce. Yawanci tsokana ce ko takura kan sa macizai harbi.
  3. Kada a rika sa hannu a cikin ramuka haka kawai
  4. A rika yawo da fitila a hannu da dare musamman ga mutanen karkara masu ratsa ciyayi cikin duhu
  5. A kula da tsabtar muhalli musamman yanke ciyayi da gyara juji a mazauninmu na cikin gari.
  6. Macizai kan ziyarci wuraren da akan samu beraye da kwadi ko da a harabar gidajenmu ne domin wadannan qananan dabbobi sukan iya zama abincinsu.
  7.  Ya kamata hukumomi su rika sa alamu na tunatarwa a wuraren da aka san ana samun macizai, a rubuta varo-varo kamar haka “HANKALI DA MACIZAI”.
  8. Da zarar maciji ya sari mutum a yi sauri a kai shi asibiti domin ba shi allurar da ta dace
  9. Kada a sa kashin dabbobi wato irin takin nan na kashin dabbobi a wurin ciwon kamar yadda wasu suke yi, don hakan zai iya sa kwayoyin cuta musamman kwayar cutar tatanas mai sa ciwon sarke hakora. Za dai a iya sa ruwa da sabulu a wanke wurin kan a isa asibiti.
  10. Kada kuma a daure saman wurin da abin ya faru don gudun kada dafin ya bi jini. Yin hakan kan iya sa wannan bangare na jikin ya mutu saboda rashin gudanar jini.
  11. Kada kuma a ce za a tsaga wurin da aska ko a ce za a zuko dafin da baki.
  12. A yanzu haka hukumomin lafiya na kasa-da-kasa kan kai alluran dafin macizai asibitocin yankunan da suke da yawan macizai, saboda a yi saurin ba wa maras lafiyar. A yankunan da ba a fiya samun sarar maciji ba sai an je babban asibiti.

HANYOYIN KARIYA DAGA HADURRAN ABIN HAWA

 

Bincike ya tabbatar da cewa hadurran abin hawa sune kan gaba wajen sanadin salwantar rayuka a kasar nan tamu, musamman a mutane da ba wani ciwo suke yi sosai ba, kamar matasa. Don haka wannan matsala ta zama annoba. Binciken ya kuma nuna cewa masu ruwa da tsaki a al’amuran yau da kullum a bangaren hadurra na abin hawa wadanda suka hada da hukumar kiyaye hadurra ta kasa, da hukumomin bada agajin gaggawa da ma’aikatan lafiya, sun tabbatar da cewa a halin da ake ciki yanzu, babu hanyar da ta fi inganci wajen kare al’umma daga wannan babbar annoba cikin gaggawa, wadda ta wuce ci gaba da fadakarwa da bayar da shawarwari a game da hanyoyin kariya daga hadarin abin hawa, saboda ganin cewa sauran matakai irin su gina hanyoyin mota masu inganci, da na jiragen kasa, ba za su samu cikin qanqanin lokaci ba.

Ko a ‘yan satuttukan nan an kiyasta cewa hadurran ababen hawa musamman motoci sun yi sanadin salwantar rayukan daruruwan mutane, wanda wannan ya sa masu fashin baqi suke ganin wadannan hadurra sun fi annobar da kwayoyin cuta kan jawo saurin kisa da jawo nakasa.

To me ke jawo hadurran?
Akwai abubuwa uku da ke jawo hadarurruka na abin hawa. Waxannan sune, a jere a muhimmanci: Mai sarrafa abin hawa (direba), shi kansa abin hawan (jirgi ne, ko mota, ko babur, ko keke), sai kuma hanyar da abin hawan ke bi.

Zai yi wahala a samu matsalar hadari idan abu ukun nan suna lafiya. Amma bincike sai ya nuna cewa babban abin da ke kawo wannan matsala shine direba. Dalilai sun hada da:
• Shan kayan maye
• Wanda kan sa tuqin ganganci
• Sai kuma tuqi ba qwarewa
• Amsa wayar salula
• Rashin duba lafiyar abin hawa kafin a sarrafa
• Mummunan lodi a abin hawa
• Rashin bincike mai tsauri akan direba kafin a bashi lasisin tuqi, musamman a yara da basu hankalta da sanin dokokin tuki ba.

Ta bangaren abin hawa, manyan ababen da ke jawo hadurra musamman akan manyan hanyoyin mota sune:
• Fashewar taya saboda rashin inganci, ko zafin kwalta. Daga nan sai
rashin fitulu (a tukin dare), da
• Rashin wiper goge ruwan sama
• Rashin sabis.

Sai kuma hanya. Matsalolin hanya sun hada da yawan samun manyan ramuka a tsakiyar titi, ko kuma rashin fadin titin da yawan samun manya-manyan tireloli masu kashe titi.

Hanyoyin Kariya Daga Wannan Annoba
Masana hanyoyin sufuri sun yi amanna babu wata hanyar sufuri da tafi kowacce rashin samun haxurra kamar hanyar sufuri ta jirgin kasa, wadda da ace ta wadata a qasar nan za a samu sauqin wadannan matsaloli. Kuma kayan masarufi za su fi saukin dauka ta wannan hanya.

Wannan ya sa dole a yabi daidaikun jihohi da suka fara aikin shigo da sabbin jiragen kasa da kuma gina hanyoyinsu, kuma ya kamata ya zama abin koyi ga sauran jihohi domin da hadurran motoci sosai. Sauran hanyoyin da akan bi wajen rage yawan hadurra sun hada da:

1. Bangaren sufuri na buqatar dokoki da dama daga majalisun dokoki na qasar nan. Misali dokokin da za su qayyade ire-iren mutanen da za a bawa lasisin tuka abin hawa, dokoki da za su tabbatar da ingancin ababen hawa, da kuma qayyade yawan shigowa dasu, da kuma dokoki da za su kula da hanyoyin sufuri masu inganci. Saboda haka ya zama wajibi a kanmu mu riqa tunatar da ‘yan majalisunmu irin dokokin da ya kamata su riqa ba wa muhimmanci.
2. Qaruwar kamfanoni masu zaman kansu na masu hannu da shuni cikin harkar sufuri na jirgin kasa, zai sa gasa a tsakanin irin waxannan kamfanoni ta yadda farashinsu zai sauko sosai.
3. A daidaikunmu kuma abubuwan da za mu kula dasu sun haxa da yawan addu’o’i kafin tuka abin hawa, da hawa doguwar hanya, tabbatar da cewa mun shiga abin hawa mai inganci, mai lafiyar tayoyi da fitulu, wanda ba a yi wa mummunan lodi ba. Sa’annan sai lura da direba yayin tafiya don kada yayi barci ko ya amsa wayar salula, ko yayi tuqin ganganci. Sai kuma daura belt din mota ko da mutum a bayan mota yake, domin belt na hana mutum bugewa a cikin mota ko hantsulowa waje, idan wani abu ya faru. Sai a kuma guji tafiyar dare.

Taimakon farko na gaggawa da zaka iya ba wadanda hadari ya ritsa dasu
Ana so a qalla kowa ya iya bada taimakon farko na gaggawa (wato first aid) ga wadanda suka shiga halin qaqa-ni-kayi kafin wani taimako daga baya yazo, domin hadari kan iya faruwa a gaban kowa, ko kuma mutum na iya zuwa ya riskeshi. Mutum zai a iya zama sanadin ceto ran wani:

1. Idan abin ya shafi mutane da yawa, a fara duba waxanda aka ga basa motsi, ko numfashi. Wato ba masu motsi ko kururuwa ake fara kaiwa dauki ba, domin da farko, rai ake ceto kafin a je kan masu ciwuka, sai dai in har an ga zubar jini sosai a masu motsin ko kururuwa.
2. A sa hannu a gefen makoshin maras motsin na dama ko na hagu, a ji ko akwai motsin bugun jini a jijiyar wuya. Idan akwai bugun jini, to yana da rai, idan kuma babu bugun magudanar jini, to a iya cewa bugun zuciya ya tsaya. Za a iya gwada farfado da bugun zuciyar idan aka fito dashi waje (daga cikin abin hawan) aka kwantar da shi kasa a bayansa. Sai a sa dunduniyar tafin hannuwa biyu, daya kan daya, a danna tsakiyar qirjinsa sau ashirin zuwa talatin, ana yi ana busa iska a bakin (duba lamba ta uku) ana kuma tava gefen wuyan ko za a ji bugun wannan magudanar jini. A yi haka kamar tsawon mintuna biyu. Idan ba bugun jinin tsawon wannan lokaci, sai a haqura ka tafi kan wani. Idan kuma aka ji bugun magudanar jini,
3. Sai a duba ko yana numfashi ko a’a. Idan ba a tabbatar ba, a sa kunne kusa da hancinsa a ji. Idan ba numfashi, a bude bakinsa a gani ko akwai abin da ya fada, don a cire. Idan kuma ba komai, a kwantar dashi a bangarensa na dama ko na hagu, saboda harshensa ya koma gefe, domin harshe ma na toshe numfashi a irin wannan yanayi. In ya fara numfashi, sai a je kan wani. Idan kuma ba numfashi, sai a daga havarsa ta kalli sama, sa’annan a toshe hancinsa, a busa iska a bakinsa, ta hanyar sa mayani tsakanin bakinka da nasa. Shima a dan yi tsawon mintina, kafin taimako ya zo.
4. Ga mai zubar da jini sosai, a yagi tufafinsa a daure masa wurin zubar jinin tamau.
5. Ga wadanda suka kasa motsa wani bangare na jiki, ta iya yiwuwa akwai karaya a wannan bangaren, ba a taba su in dai suna numfashi har sai ma’aikatan lafiya ko na hukumar ba da agaji sun zo da kayan ceto.
Idan an samu dama, duk sai an yi wadannan kafin a kama hanyar asibiti.

HANYOYIN KARIYA DAGA ZAZZABIN LASSA

Zazzabin Lassa wani ciwo ne da kwayoyin cutar virus ke kawowa. Su kuma wadannan kwayoyi beraye ne ke yada su. Bayanai sun nuna cewa, an fara samun bullar cutar zazzabin Lassa ne a kauyen Lassa dake jihar Barno, a arewacin Najeriya, shekaru fiye da hamsin da suka gabata.

A cikin wadannan shekaru, cutar ta samu bulla wasu kasashen a yammacin Afirka, wato kasashe irinsu Guinea da Saliyo da kuma tsakiyar Afirka. Alkaluma dai suna nuna cewa, mutane fiye da dubu 300 ne kan kamu da zazzabin Lassar a kowace shekara a duniya.

Bincike ya nuna cewa, an gano bullar cutar ne, yayin da wata malamar asibitin koyarwa na jami’ar Fatakwal ta kamu da zazzabin, wanda kuma ya zama ajalinta.

Daga bisani kuma an gano wasu mutanen da suka kamu da cutar .

A yanzu haka kuma ana samun bullar cutar a garuruwa irinsu Taraba da.

 

Ta yaya ake kamuwa da ciwon?

Beraye sukan yi yawo a gidajenmu su je neman abinci musamman da dare. Wasunsu a irin wannan lokaci sukan kwaso wadannan kwayoyi na virus. Wasu sukan hauro ta katanga, wasu sukan shigo ta rariya, wasu kuma ma suna da ramuka cikin gidajenmu. Idan suka taba abincin da yake a bude, sukan iya sa mana wadannan kwayoyi abinci, mu kuma mu dauka in mun ci. Wasu lokuta ba sai sun taba mana abinci ba, kashinsu da fitsarinsu kan iya yada kwayoyin cutar ta hanyoyin numfashi idan muka shaki warin.

Ana kuma iya daukar ciwon ta hanyar taba jikin mai ciwon, musamman a ma’aikatan asibiti.

 

Alamomin ciwon

Akwai zazzabi, sai ciwon ciki da amai da gudawa, wadanda za a iya ganin jini a ciki. Babu inda ciwon bai iya tabawa, domin za a iya jin kasala, ciwon kai, tari, mura da dai sauransu. Don haka babu dai takamaimai wata alama guda daya da za a danganta ciwon da shi.

 

Hanyoyin Kariya

1. Kada a rika bari beraye suna samun sukuni a cikin gidajenmu; a nemi ramukansu a tottoshe musamman a dakunan da ake ajiyar abinci wato store; a kuma kawo mage cikin gidan.

2. A daina barin abinci a bude ko da yaushe ya zama a rufe, kada wani abu ya shiga

3. A daina barin kwanukan abinci suna kwana ba wanki. Mun san yawancin gidajenmu akan bar wanke-wanken kwanuka zuwa da safe, wanda hakan kan iya jawo beraye su hau kwanukanmu cikin dare. Ko da an yi wanke-wankenma, a dauraye su sosai kafin a zuba abinci

4. Idan an yi wanke-wanke a share guntattakin abinci sosai, kada a bari su shiga rariya, don gudun kada ya jawo beraye.

5. Idan an ga fitsari da kashin beraye kada a share sai an sa kyalle an rufe hanci tukuna

6. Idan an ji zazzabi da ya wuce kwana biyu, ko ya ki jin magani, a garzaya asibiti

7. Idan ana da maras lafiya wanda ake tunanin yana da wannan ciwo, kada a rika taba shi sosai ko amansa, a sa leda a hannu kafin a yi aikin amai.

GWAJIN KWAYOYIN HALITTU NA DNA


An kirkiro wannan gwaji ne na DNA testing a shekarar 1984 a Jami’ar Leista a Ingila. Ana iya amfani da wannan gwaji wajen gano iyayen mutum ko gano wani mai laifi ko wanda kamannin fuskarsa suka sauya misali.

Kwayoyin DNA sune halittu mafi kankanta a jikin dan Adam domin suma a can cikin kananan kwayoyin halittu na cells suke. Kowane dan Adam yana da kwayoyin kusan iri daya da sauran mutane amma yanayin malkwayar halittun kan iya sa masana gane inda na wani ya bambanta da na wani ta hanyar tarasu da yawa a yi nazari a kansu. Dole sai ana da wadannan kwayoyin halittu na mutum a ajiye a matattara tukuna kafin a iya amfani da gwajin. Ana samun wadannan kwayoyi ne a jini, miyau ko a gashi sai a ajiye su a matattarar bayanai, ta yadda da zarar bukatar amfaninsu ta taso za a yi amfani dasu. Idan ba a samu a jini ba ko halittun jikin mutum ba, akan iya samu a jikin wani abu da mutumin kan yi amfani da shi kamar burushin wanke baki ko kum na taje kai.

Wannan gwaji yana kama da gwajin zanen dan yatsa (fingerprinting test) dan bambancin kawai shine cewa babu mutane biyu a duniya masu zanen ‘yan yatsu iri daya ba. (Shi ya sa alal misali ake cewa duk wanda ya yi rijistar zabe sau biyu, na’ura mai kwakwalwa za ta gane, wanda hakan ya sa hukumar zabe ta goge sunayen wadanda suka yi rajista sau biyu. Hakan ta sa wasu suka je wurin zabe basu ga sunansu a rijista ba. Duk da cewa kuma bayanai sun nuna cewa wasu sau daya kawai suka yi rajista amma aka yi dan kure aka goge nasu sunan a rajista. Hakan nan kuma hukumar zata iya gane mutumin da yayi rijista sau daya amma ya dangwala kuri’u fiye da guda ta hanyar wannan na’ura cikin sauki duk inda yake kuwa. Akwai bayanai masu nuna cewa yanzu an fara bi ana kamo irin wadannan mutane daya bayan daya.) Banda laifi na zabe a yanzu duk wanda yayi wani laifi kamar sata, fashi, fyade da sauransu in dai har wannan inji na hukumar zabe ya dauki hannunsa to za a iya gano shi cikin sauki, domin akwai bayanan cewa hukumar zabe za ta iya bawa hukumar ‘yan sanda wadannan bayanai domin yakar laifuffuka. Wannan gwaji kenan yana da matukar amfani wajen rage laifuffuka a cikin kasa.

To haka ma gwajin kwayoyin halittun DNA, wato za a iya dauka a jikin mutum ko yana sane ko baya sane ko a abinda yake amfani dasu na yau da kullum kamar yadda muka zayyana a sama, a kuma ajiye su sai bukatar amfaninsu ta taso.

A halin da ake ciki yanzu akwai irin wannan matattara ta bayanan kwayoyoyin halittun dan Adam da dama a duniya. Ba na jin muna da ita a wannan kasa. Mafi girma dai daga cikinsu itace wadda gwamnatin Amurka take kula da ita wadda ta kunshi bayanan kwayoyin halittun kusan mutane miliyan biyar, wanda da yawansu ma basu san Amurkan tana wadannan bayanai nasu ba.

ALLURAN RIGA-KAFI

Yara ýan kasa da shekara biyar sun fi mu shiga hadarin kamuwa da cututtuka saboda dalilai biyu. Na farko shine kwayoyin garkuwar jikinsu bata yi kwarin da za ta yaki cututtuka ba, na biyu kuma shine saboda kusan komai suka samu ko suka taba baki suke kaiwa, inda nan ne hanyar da mafi yawan kwayoyin cuta ke shiga jiki. Wannan yasa alkaluma kuma suke yawan nunawa cewa kananan yara ýan kasa da shekaru biyar sun fi kowa mutuwa. Dalilin da ya sa aka fi ba da muhimmancin riga-kafi a kan kananan yara kenan.

Su dai magungunan riga-kafi wasu sindarai ne da ke sanya jiki kera kwayoyin garkuwar jiki da za su iya yakar cuta. Wato dai kamar makarantar koyon aikin soja take, wadda ke dauka kuma take yaye sojoji dabam-dabam, na kasa, da na ruwa, da na sama. Misali sinadarin riga-kafin cutar tarin fuka tana samar da sojojin kare yaro daga tarin fuka, sinadaran riga-kafin ciwon shan inna, na samar da sojoji daban na yaki da kwayoyin cutar shan inna. Duk cutukan da suke da alluran riga-kafi za a ga cewa kwayoyin cuta ke kawo su, wanda sune suka fi addabar kananan yara. Cutar amosanin jini da ke addabar wasu yara misali, ba a yakarta ta hanyar allurar riga-kafi saboda ba kwayoyin cuta ke jawo ta ba sai ta hanyar gwajin saurayi da budurwa kafin suyi aure.

Ba za mu gane amfanin alluran riga-kafi ba sai idan mun tuna da wasu cutuka biyu da suka addabe mu a zamanin da wadanda yanzu kusan aka daina jin duriyarsu. Wadannan cutuka sune ciwon agana (smallpox) da tarin shika ko tarin jaki (whooping cough). Ciwon agana ma an daina jinsa ako ina cikin duniya, amma akan dan ji bullar tarin shika jefi-jefi a wasu yankunan na duniya. Ba don zargin da ya taso na cewa an gurbata allurer shan-inna ba da tuni ciwon shan innan ma an manta dashi. Ciwon tarin fuka (TB) a kanan yara shima ya ragu matuka saboda lambar nan ta BCG. Ana nan ana kuma kera sinadaran alluran riga-kafin zazzabin cizon sauro da na cutar kanjamau.

 

Ga jadawalin alluran da ya kamata yaranmu su samu tun daga haihuwa:

 

Lokaci Allurar Riga-kafi
Ana haifar yaro akwai allura daya da digon-baki daya Lambar BCG ta tarin fukada Hepatitis B ta ciwon hanta

da digon-baki na OPV ta shan-inna

Idan ya cika wata daya akwai allura daya da digon-baki daya Allurar DPT ta tarin shika da sarke-hakoraDa digon-baki na OPV
A wata na biyu akwai allura daya da digon-baki daya A sake allurar DPT da OPV
A wata na uku akwai allura daya da digon-baki daya A sake kaishi allurar DPT da OPV
A wata na tara akwai allura daya da digon baki daya Allurar kyanda da digon-bakin sinadarin Vitamin A
A wata na goma sha biyar akwai digon-baki daya Digon-bakin sinadarin Vitamin A
Duk bayan shekara goma Allurar sarke hakora ta Tetanus
Duk shekara lokacin zafi Allurar sankarau ga wadanda ke cikin hadarin kamuwa

 

 

HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON KWALARA

Ciwon kwalara ko kuma ciwon amai da gudawa kamar yadda aka fi sani, ciwo ne da idan aka daure aka bi shawarwarin masu aikin lafiya, ba wanda zai kamu dashi. Kasashen da suka ci gaba suma sun yi fama da irin wannan ciwon amma yanzu sun shawo kansa. A yanzu an fi ganinshi a irin kasashenmu inda duk shekara sai ciwon ya halaka miliyoyin mutane, akasarinsu kananan yara. Kwayoyin cutar bacteria da ake kira Vibrio cholerae, su ke kawo shi. Dole ayi magana akan wannan ciwo domin ko a rage mace-macen da ciwon ke kawowa.

Yaya ake kamuwa, yaya kuma ake gane alamun ciwon?

Kwayoyin cutar suna rayuwa ne a gurbataccen ruwa wanda idan aka sha, sukan je su makale a jikin ‘ya’yan hanji. Nan da nan cikin yini guda sai amai da zawo mai hade da majina, ba ciwon ciki. Kafin gari ya waye mutum ya fada, ba kuzari, ruwan jikinsa ya kare. Idan ba a dauki mataki ba ya cika. Idan babba ne akan dau lokaci kan ya galabaita. Yara ‘yan shekara 1-5 da haihuwa da tsofaffi su suka fi kamuwa. Manya sukan iya kamuwa da kwayar cutar ba tare da sunyi amai ko zawo ba.

Ciwon na yaduwa ne kamar wutar daji ta hanyoyi uku: Kuda yakan dauko kwayoyin cutar a amai ko zawon da mai cutar yayi, ya taba abinci ko ruwa. Hanya ta biyu kuma mutum ya taba amai ko zawon mai cutar ya ci abinci bai wanke hannu ba. Hanya ta uku shine idan mai dauke da kwayar cutar yayi ba haya ko zawo kusa da ruwan da jama’a ke amfani da su wato ko rijiya ko kogi.

Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo?

  1. Da zarar an ga alamun ciwon, a samo ruwan gishiri da sukari na sachet wato ORS a hada a fara ba mara lafiya kafin a garzaya asibiti mafi kusa. Idan ba a samu ORS ba a samu gishiri cikin karamin cokali daya da sukari cikin karamin cokali goma a hada a ruwa mai tsafta kwatankwacin kofi biyu, a bayar a hankali har a kai asibiti
  2. Dole a tafi asibiti domin karin ruwa saboda mara lafiya zai iya amai ya dawo da ruwan gishirin da aka bashi
  3. A asibiti akwai kwayoyin magunguna na riga kafi da ake ba wadanda wani na kusa dasu ya kamu da wannan ciwon
  4. A tabbatar an tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha. Ruwan famfo yana da sinadarin chlorine da kan kashe kwayoyin cutar
  5. Hukumomin gidan ruwa su tabbata an saka sinadarin chlorine yadda ya kamata kafin a sako ruwa
  6. A guji sayen kankara da ba a tabbatar daga ruwan da aka hadata ba
  7. A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan gida da kuma kafin cin abinci. Yawan wanke hannu da sabulu yana hana kamuwa da wannan ciwo kwarai da gaske
  8. A rufe duk wani abinci da abin sha don kada kuda ya hau
  9. A kiyaye tsabtar muhalli don kada kuda ya samu wurin zama
  10. Kar a ci kayan lambu irin su latas da karas da ba dafasu ake yi ba, musamman a irin wannan lokaci.
  11. A guji yin bahaya a kusa da magudanan ruwa ko rijiya ko kogi

HANYOYIN KARIYA DAGA YOYON FITSARI


Muna so mu san me ke kawo yoyon fitsari? Kuma ya za a kiyaye shi?

-Shu’aibu Ubale Freedom

Abubuwan da kan kawo yoyon fitsari guda uku ne, doguwar nakuda, da yiwa mata kaciya da kuma yiwa mata yanka ko kari yayin haihuwa. Doguwar nakuda takan faru sanadin abu biyu; imma dai kugun uwar matsattse ne, ko kuma kan jariri kato ne. Idan kugun uwa matsattse ne ko dan karami kuma kan jariri daidai yake, to kugun zai rike kan jariri ya kasa fitowa. Hakama idan kugun uwa daidai yake wato wadatacce ne amma kan jariri kato ne, to kan jariri zai makale ya kasa wucewa. Idan dayan biyun ya faru, maimakon mace tai nakuda cikin ‘yan awoyi, sai ta yini ta kwana, wato nakuda ta zama doguwa kenan. To wannan yakan sa kan jariri ya rika gogar fatar da ta raba mafitsara da wurin haihuwar ta koke, fitsari ya fara yoyo, kuma a mafi yawan lokuta akan rasa jaririn saboda wannan matsi.

Ana iya kare aukuwar haka tun daga fara zuwa awon ciki inda za a iya sanin girman jariri har zuwa haihuwa a asibiti. Idan mace bata son haihuwa a asibiti to yana da kyau ta kira kwararriyar ungozoma wadda aka ba horo na zamani. Ita wannan ungozoma ta san lokacin da yakamata nakuda ta kare, ta kuma san lokacin da dole sai an rankaya asibiti don yin tiyata a cire jariri kafin ya rasu ko kuma kafin yoyon fitsari ya auku. Har ila yau ita wannan mata ta san daidai inda akewa mata kari ta yadda ba zata yanks mafitsara ba.

Hanya ta uku ta samun yoyon fitsari itace ta yiwa mata kaciya ko yankan gishiri ko angurya da wasu wanzamai ke yi, inda cikin kuskure suke taba mafitsara da aska hart a huje fitsari ya fara yoyo. Ana iya kare aukuwar haka idan aka daina yankan gishiri kwata-kwata.

Duka dai a yanzu ana iya gyara ciwon yoyon fitsari kusan a kyauta, amma dai an ce riga-kafi yafi magani.

Wane wata ne mai ciki ya kamata ta fara zuwa awo? Kuma me ke kawo ciwon ciki mai tsanani a watannin ciki na farko?

-H. Umar

Da zarar mace tayi batan wata ake fara zuwa awo. A nan ne za a tabbatar ko ciki ne ko ba ciki bane ta hanyar gwajin fitsari. Bayan kamar wata biyu kuma ana sake komawa don ayi hoton ciki, musamman ma idan akwai ciwon ciki mai tsanani domin a gani cikin a mahaifa yake ko a wajen mahaifa.

Ina da ciki wata bakwai amma ciwon kafa da rikewar jijiyoyin kafa da ciwon kugu da na mara sun dameni me kawo haka?

-Safiya A, Samaru da wata baiwar Allah

Wadannan alamu ne na cewa cikin da yayi nisa, kamar yadda kika fada wata bakwai zuwa haihuwa saboda girman jariri da motsinsa. Wadannan alamu sun fi tsanani a cikin fari, wato idan ciki na biyu ya zo zasu zo da sauki, haka ma sauki zai karu a na uku har ki saba. A cikin farko kusan ba makawa sai kin sha wannan ‘yar wahalar kuma wani zubin paracetamol da sauran magungunan ciwon baya basa magani. Abinda yafi magani shine tausa. Wato mai gidanki ya rika yi miki tausa a kafa da baya da kugun wani lokaci da ruwan dumi wani lokaci da hannu.

Me yasa wasu mutane ke yin tika bayan sun ci abinci kamar yadda dabbobi suke yi?

-Bashir Ibrahim Fatakwal da Abdurrashid Yakubu da Abdullahi Tenten Amaco Foam

Idan dabba taci abinci takan koma gefe ta kwanta ta rika fito dashi kadan-kadan tana taunawa a hankali har yawu ya narkar dashi kafin ya bi uwar hanji, saboda cikinsu bashi da karfin sinadarai na asid masu narkar da abinci.

Tabbas akwai wasu daidaikun mutane da suke yin tika kamar dabbobi, wato bayan sun ci abinci sai kadan daga ciki ya rika dawowa wuya zuwa baki kafin daga baya su kara taunawa sannan su hadiye ko su tofar (rumination syndrome). Ana ganin kamar irin tunbudi (ba amai ba) wanda jarirai keyi shi ke bin mutum idan ya manyanta. A wannan yanayi babu yunkurin amai ko ciwon ciki, sai dai ‘yar rama idan mutum ya fiya yi. Don haka ba a cika bad a wasu magunguna don magance wannan matsala ba, domin magungunan nasara basa iya hana wannan yanati aukuwa. Shawarar da aka fi ba masu yi itace ta yin numfashi da ciki maimakon da kirji duk bayan cin abinci don abincin yayi saurin wucewa kada ya dawo wuya.

Tunanina ya kasa fahimtar abinda taba sigari ke karawa jiki. Ko za ka yi min bayani akan amfaninta da illarta da kuma maganinta?

Ashir, Richifa

Duk da cewa masu shanta suna jin dadinta sosai ita taba sigari bata karawa jiki lafiya. Amma tabbas tana karawa jiki lahani. Abinda yasa ba’a rabuwa da ita duk da rashin karawa jiki wani abu da take yi shine saboda sinadarinta a kwakwalwa yafi aiki. Wannan sinadari shine nicotin, wanda banda kwakwalwa yakan iya yiwa zuciya illa da magudanan jini da fatar jiki lahani. Akan iya ganin taruwar wannan sinadari a fatar mai shan sigari ta yadda za a ga fatar tayi baki. To hakama duk sauran sassan jiki da ba a iya gani ke kasancewa, wanda zai sa a hankali su mutu.

Daya illar kuma ta taba sigari itace ta hayakin. An yi amanna cewa wannan hayakin ne kawo ciwon daji na huhu. Illar hayakin bata tsaya kan mai sha kawai ba a’a har wanda yake wurin idan ana sha. Misali idan mai gida na shan taba a cikin gida to duk mutanen gidan wadanda suka ji warin tabar kamar sun sha ne. Wasu likitoci suna ganin kamar hayakin bayawa mai sha illa kamar yadda yakewa na kusa dashi tunda hayaki yawo yake. Hakan yafi illa kuma ga kwakwalwar kananan yara dake wurin ko yaron dake ciki idan mace mai juna biyu na wurin da ake busa hayakin.

Da yake tana zama kamar alakakai kadangaren bakin tulu (ka daina ta sa ka ciwo, ka ci gaba shima ciwo) saboda wancan sinadari mai aiki a kwakwalwa, barin shan taba na da wuyar gaske. Mai son ya daina zai iya zuwa ya nemi wani cingam mai dandanon nicotin don ya rika taunawa. Wannan zai sa yaji a ransa kamar nicotin din yake zuka har idan akai sa’a ya manta da sigarin.

Ni an cire min tsakuwa a koda har sau biyu kuma na karanta a hanyoyin kariya daga ciwon koda a wannan mujalla inda naga kace a rage cin jan nama da alaiyahu da kofi. To naman har da na kaza? Ina son karin bayani

-Muhd Baba, Gombe

E yawan cin nama musamman a irinku wadanda aka cirewa tsakuwa ko a koda ko a matsarmama kan sa tsakuwar ta sake taruwa saboda sinadarin uric acid wanda kan dunkule ya zama tsakuwa. Kuma naman har na kaza da kifi. Abinda nace shine a rage yawan ba daina ci dungurungum ba. A irin kasashenmu irin cin nama da muke yi yanka daya ko biyu a cikin abinci ba zai zama hadari ba. Hadarin shine idan kai da aka cirewa tsakuwa kana ci da yawa kamar irin na lokacin laiya da babbar sallah, to zai iya sa tsakuwa sake taruwa, amma ba cin yanka daya ko biyu a rana ba. Idan kaci naman to ka tabbata duk inda ka shiga a wannan ranar sai ka sha ruwa don yayi saurin wanke wancan uric acid a fitsarinka. Alaiyahu da kofi suma suna sa tsakuwa mai sinadarin oxalate taruwa a irinku.

Sauran mutane wadanda ba a taba cire musu tsakuwa ba ko kuma ba wasu a danginsu na kusa da aka taba cirewa za su iya ci ba matsala.

Ni kuma gidana da motata da ofis duk akwai na’urar sanyaya wuri ta AC. Anya babu illa kuwa ga lafiyata, idan akwai kuma ya zan kare kaina?

-Nasir Ibrahim Jagoran Falasdinawa

Idan dai ana yiwa nau’rar sabis akai-akai to ba wani hadari a irin yanayinmu na zafi. Domin bayan sanyaya wuri na’urar AC takan tace kwayoyin cuta dake cikin iska wadanda idan aka shaka kan iya zama lahani. Yin sabis akai-akai don wanke wadannan kwayoyin cuta da nau’rar ta tara daga ciki zai rage yawan mura da takan jawo.

HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR KANJAMAU


Ina son cikakken bayani a game da cutar kanjamau (HIV/AIDS). Shin za a iya daukar ciwon bayan an sadu da mai dauke dashi sau daya kawai? Za a iya dauka idan wani ruwan jikin mai cutar ya taba mutum? Mene ne alamun ciwon? Kwanaki nawa kwayar cutar ke dauka kafin ta bayyana a awon jinin mutum don idan mutum yayi gwajin akan ce ya sake dawowa bayan watanni a sake.

-Sani Musa da Basira Azare

Cutar kanjamau ciwo ne da kwayoyin cuta na virus ke kawowa. Wadannan kwayoyin cuta ba kamar na bacteria ba, suna da wuyar sha’ani, domin suna hayayyafa fiye da yadda wani magani zai yi musu tasiri. Wato ana hayayyafarsu suma ‘ya’yan suke kara hayayyafa kamar kiftawar ido. Wannan itace kwayar cutar HIV. Kwayoyin kan mamaye kwayoyin garkuwar jiki ko sojojin jiki. Ciwon da suke sawa kuma shine AIDS wato mutuwar wadannan sojoji na jiki.

Yadda ake daukar kwayar cutar:

Hanyoyi hudu da aka tabbatar ana daukar ciwon sune;

  1. Saduwa da mai ciwon,
  2. Karin jini mai dauke da kwayar cutar
  3. Daga uwa zuwa jaririnta.
  4. Daga kayan kaifi

Saduwa da mai ciwon ko da sau daya ne da mu’amala ruwan jikin mai ciwon kamar miyau zai iya sa wanda bai da ciwon ya kamu, musamman idan akwai ciwo ko miki a daidai wurin saduwar ko kuma a inda ruwan jikin mai ciwon ya taba. Za a iya kamuwa bayan saduwa ko da kuwa an sa kariya domin kwayoyin cutar sukan iya bi ta kananan kofofin robar, don sun fi kofofin duk wata kariya kankanta. Idan da kariya, to akan iya rage hadarin kamuwa daga kashi 100 zuwa kashi 90. Shi yasa ake so ayi gwajin jini kafin auratayya. Mai dauke da cutar ba zai auri maras cutar ba, sai dai dan uwansa mai cutar.

Sai kuma karin jini da ake wa wasu ba tare da an gwada jinin ba. Akwai masu dauke da wannan ciwo da dama da suka kamu da wannan ciwo saboda irin wannan kuskure. To wani ya ce sauro da ke zukar jinin mutane ya dura wa wasu me ya sa baya sawa mutane? To bincike ya nuna kwayar cutar mutuwa take a cikin sauro ba kamar ta maleriya ba.

Ita kuma hanya ta uku, wato daga uwa zuwa jaririnta, na iya faruwa tun jariri na ciki, ko kuma yayin haihuwa ko kuma ya dauka yayin shayarwa.

Hanya ta hudu, wato ta kayan kaifi, na faruwa ne yayin da aka yi amfani da reza, aska, kaho ko allura wadda mai kwayar cutar yayi amfani dasu.

Ba a iya dauka don kawai an zauna da mai ciwon ko an taba jikinsa ta mu’amala ta yau da kullum kamar gaisuwa ta musabiha da sauransu.

Alamun Ciwon:

Shigar kwayar cutar jikin mutum ba lallai ne yazo da wata alama ba, don sai mutum yakai shekaru goma ma yana dauke da kwayar cutar amma bata kawo masa ciwon kanajamau ba. Wadannan sune masu yawan sojojin jiki. A wasu mutane kuma marasa karfin garkuwar jiki da kananan yara, watanni ne kawai kwayar zata yi a jikinsu su fara nuna alamu.

Alamun sune a ga mutum yana rama wata da watanni kuma yana cin abinci kamar kowa, ko gudawa wato zawo wanda yaki jin magani tsawon satuttuka, ko a ga yana tarin da yaki jin magani shima na tsawon satuttuka sakamakon cutar TB wadda tafi kamasu. Hakanan duk da cewa tarin TB shine babbar alamar ciwon kanjamau a irin kasashenmu, ba lallai bane kuma mai tarin TB ya kasance yana da ciwon. Wadannan sune manyan alamu amma akwai kuma sauran alamu da dama. Wato duk wani ciwo da yaki ci yaki cinyewa, zai iya kasancewa sanadiyarsa shine ciwon kanjamau.

Gwajin jini:

Akwai cibiyoyi na gwajin jini kyauta a wurare da dama don sanin ko mutum na dauke da wannan ciwon ko a’a. Yana da kyau kowa ya san ko yana dauke da wannan ciwo ko kuma akasin haka. Amma wadannan rukunin mutane da zan lissafo dole ne suje a yi musu; idan mutum na shirin sabon aure, ko kuma mai auri-saki ne, ko wanda aka taba yi masa karin jini ko lafiyayyen mutum wanda yaje kai gudunmowar jini asibiti aka ki daukar nasa, ko wanda ake yawan yi masa amfani da kayan kaifin da ba a tsabtace su ba, ko kuma yaron da iyayensa ke da ciwon. Amfanin gwajin kafin cutar ta bayyana yafi yawa nesa ba kusa ba fiye da idan cutar ta bayyana.

Idan alamun cutar basu bayyana ba aka yi gwajin jini aka ga kwayar cutar, to sai an yi masa wani gwajin a mataki na biyu a ga ko yana bukatar magungunan da zasu rage yawan kwayar cutar a jikinsa ko kuma shawarwari kawai yake bukata na yadda zai yi rayuwa kamar kowa. Idan kuma akayi gwajin jini ba a ga cutar ba, a wasu lokuta akan ce mutum ya dawo bayan wata shida a sake gwadawa don dai a tabbatar. To duk wanda akayi masa wannan gwajin sau biyu aka babu, to kusan a iya cewa baya dauke da kwayar cutar. Gwajin cutar na ELISA wani gwaji ne da ba a yinsa kyauta saboda tsadarsa kuma ana yina sau daya kawai zai nuna mutum na da ciwon ko babu. A wasu lokuta a asibiti idan mutum yaje ba da gudunmowar jini aka dau nasa bayan anyi wani gwaji to kusan bai da ciwon kenan don gwajin kwayar cutar kanjamau (HIV) da na hanta (hepatitis) akeyi dama.

Hanyoyin kariya:

  1. Kamewa har sai anyi aure
  2. Tabbatar an yi gwajin cutar ga wanda za ka/ki aura kuma a nuna takardar shaida kafin a daura auren
  3. Tabbatarwa cewa jinin da za a karawa mutum an gwada shi a asibiti
  4. Awon mata masu juna biyu
  5. Ka tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko an kona su da wutar lighter ko an wanke su da sinadarin bleach kafin ayi maka amfani dasu
  6. Zuwa cibiyoyin gwaji don sanin matsayin mutum na taimakawa rage yada ciwon

Follow

Get every new post delivered to your Inbox.